Makarantar isilamiyya ta Dausayin Larabci da Darussan Musulunci ta roki Al’ummar musulmi da masu ruwa da tsaki har ma da Gwamnatoci ci da su tallafa mata domin samar mata matsuguni na din-din-din don cigaban harkokin addinin musulunci da bunkasa harshen Larabci.
Darakta kuma mamallakin Makarantar Sheik Yahaya Abubakar Yahaya (Malam Bala) ne ya bayyana hakan ne lokacin saukar karatun alqur’ani Mai girma karo na Farko na Dalibai goma (10) a harabar makarantar dake Unguwar Hotoron Arewa cikin Karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, Arewa maso yammacin Nigeria.
Ya ce matukar makarantar ta sami matsuguni nata na kanta hakan zai tallafa wajen bunkasar tadarussan da ake koyarwa a ciki.
“Duk inda aka samu nasarori dole akwai kishiyoyyin su, matsaloli da muke fuskanta baza su wuce na Muhalli namu na kammu ba, ya zama Makarantar mu muka samu tamu ta kanmu ba muna Dan rabe ne a wata makarantar ba, kaga makarantar da muke karatu ta Boko ce sai a Asabar da lahadi muke samu muyi amfani da ita ko kuma idan sun tashi da yamma.” Inji Malam Bala.
Ku Cigaba da Karatu: Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC
“Ko da makarantar ta wa ce dukka to sai kaji wani bangare yana zargar wani bangare da batawa ko lalata makarantar, misali akwai abokanai na makarantar tasu ce, amma sai kaji a mafi yawan lokaci bangaren Boko yana zargin bangaren isilamiyya da Bata wani bangare na makarantar.” A cewar Bala.
Malamin daga nan ya roki iyayen yara da su rika bibiyar harkokin karatun ‘ya’yan su tare da tabbatar da biyan Kudaden makarantar da ake karba wanda basu taka Kara sun karya ba idan akayi la’akari da wasu makarantun.
A jawabinsa, babban bako Mai jawabi, kuma tsohon kwamandan kungiyar tsaro da kare dukiyoyin al’umma na Arewa maso yammacin Nigeria Muktar Faris Hotoro ya bayyana takaicin sa kan yadda wasu iyayen ke zubawa ‘ya’yan su Ido suna abin da suka ga dama ta yadda wasu Yan matan na zama a cinyar samarin su ko jikin daya yana gugar na daya a lokacin da suke zance.
Ya ce kungiyar ta Vigilantee da Dagacin Hotoro da ma hukumar Hisba ta yankin sun dauki damba na yakar matsalolin ko rashin da’a da wasu daga cikin matasa ke aikatawa.
A yayin saukar Malam Ibrahim Dan-sheka, sannen malamin addinin musulunci a yankin yayi wa Dalibai darasu da kuma Jan hankalin iyayen domin kula da ilimin ‘ya’yan su gami da biyan Kudin makaranta akan lokaci.
Ku Karanta: Ba Mu Ce Bamu Da Karfin Buga Sabbin Kudi Ba — CBN
Wasu daga cikin daliban da suka zanta da GLOBAL TRACKER wadanda suka hadar da Zakariyya Sale Sabo Kaugama da Zainab Adam Abubakar sun bayyana farin cikin su gami da Jan hankalin ‘yan uwansu Dalibai da su cigaba da jajircewa a Neman ilimi.
Dalibai 10 ne dai sukayi saukar wadanda suka Hadar da Zakariyya Sa’ad Shehu da Zakariyya Sale Sabo (KAUGAMA) da Jamila Garba da Zainab Adam Abubakar da Hauwa’u Idris Adam da Amina Yusha’u Idris da Hajara Ya’u Idris da Amina Yahaya Adam da Maryam Shehu Sunusi da kuma Khadija Shehu Sunusi.
Allah yabada ikon taimakawa