Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamitin miƙa mulki, wadda za ta gudanar da shirye-shiryen miƙa mulki zuwa wata sabuwar gwamnatin da za a zaɓa cikin wannan wata.
Shugaban wanda sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya wakilta ya ce dole a rika tuna ci gaban da gwamnatinsa ta samar.
A makon da ya gabata ne shugaban shugaban ƙasar ya amince da kafa kwamitin tare da sanya hannu kan dokar ta ta samar da kwamitin, domin halasta ayyukansa.
Ku Karanta: Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC
Shafin internet na BBC ya rawaito cewa yayin da yake rantsar da ‘ya’yan kwamitin Boss Mustapha ya ce hakan wani abu ne na tarihi da gwamnatinsu ta samar wajen nuna yadda ta damu wajen bunƙasa harkokin dimokradiyya a ƙasar.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki ne dai ‘yan Nigeria za su zaɓi sabon shugaban ƙasa na gaba, da zai gaji kujerar shugaba Buhari.
Inda kuma za a miƙa mulki ga sabuwar gwamnatin ranar 29 ga watan Mayun shekarar da muke ciki.