Daga: Sabo Suleiman Jigirya
Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce Sanya mata a harkar siyasa da kuma basu manyan Mukamai zai karawa musu gwarin gwiwar shiga Siyasa da cigaban al’umma.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da uwar gidan dan takarar shugabancin kasar nan na jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu Sanata Oluremi Tinubu ta ziyarce shi a fadar sa.
Ado Bayero ya ce ziyarar da uwar gidan dan takarar ta kawo jihar Kano zai basu damar zama da mata domin jinkoken su.
Ya Kuma Kara da cewa la’akari da irin mukamin da take da shi hakan ya sa ta zama gogaggiya a harkokin Siyasa da nufin Bada gudun mowa a cigaban Yan Nigeria.
Ku Karanta: Yanzu–Yanzu: Wellcare Ya Nemi Afuwar Gwamnatin Kano Bayan Rufe Shi.
Da take nata jawabin, Sanata Remi Tinubu ta ce ta kai ziyara jihar Kano ne domin ganawa da kungiyoyin mata da Kuma ziyartar Masarautar Kano.
A yayin ziyarar, Miss Tinubu tana tare da Mai dakin Dan takarar mataimakin shugaban kasa Kashim Shitima da uwar gidan gwamnan jihar Kano Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje.