• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Karancin Kudi ya sa JAMB Kara Wa’adin Rejista.

ByGlobal Tracker

Feb 15, 2023

Sakamakon yadda Yan Nigeria suka shiga tasku na karancin Kudi da matsalar man Fetir, hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire a Najeriya (JAMB) ta ƙara wa’adin rajistar jarrabawar wannan shekara zuwa mako ɗaya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dakta Fabian Benjamin ya fitar ya ce zuwa ranar Talatar da ta gabata hukumar ta samu mutane 1,527,068 da suka yi rajistar jarrabawar, ciki har da ɗalibai 168,748 da suka nuna sha’awarsu ta yin jarrabawar gwaji wato Mock-UTME.

Ya ƙara da cewa hukumar ta faɗaɗa ƙarfinta, ta yadda take yi wa mutane 100,000 rajista a kowacce rana.

Hukumar ta ce ta ƙara wa’adin ne saboda wahalhalun da ɗalibai ke fuskanta wajen samun kuɗin rajistar, da kuma matsalolin amfanin da tsarin banki ta internet wajen sayen lambobin rajistar a yanar gizo.

Ku Karanta: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano

JAMB ɗin ta ce za a ci gaba da sayar da lambobin rajistar har zuwa ranar Litinin, yayin da rajistar za ta ci gaba har zuwa ranar Laraba 22 ga watan Fabrairun da muke ciki.

Tun da farko dai hukumar ta JAMB ta sanya ranar 14 ga watan na Fabrairun a matsayin ranar da za ta rufe yin rajistar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *