• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Masarautar Gaya Jigo ce a Cigaban Al’umma – Ibn-sina

ByGlobal Tracker

Feb 16, 2023

Daga: Jamila Suleiman Aliyu

Hukumar hisbah ta jihar Kano ta bayyana masarautar Gaya a matsayin Jigo a cigaban Al’ummar Kano ta Kudu da ma jihar Kano ba ki daya.

Babban kwamandan hukumar Aheik Haroon Muhd Sani ibn-sina shine ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da hukumar hisbah ta kaiwa masarautar ta Gaya.

Ya ce masarautar tana bada gudun mowa domin cigaban ayyukan addaini tare da samar da zaman lafiya da taimakawa marasa karfi.

Haroon Ibn-sina ya bayyana sarkin gaya a matsayin jagoran al’umma kuma na gaba-gaba a iyayen Al”umma a jihar kano saboda yadda yake baiwa hukumar damar da ta kamata a fannin aikin su na Hisbah.

Ku Karanta: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano

Kwamandan Hisbar ya kuma roki masarautar data sa baki ta hanyar yin kira ga mawadata dasu taimakawa masu karamin karfi duba da yanayin da ake ciki.

A nasa jawabin sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim ya yaba da ziyarar ta hukumar hisbah tare da yaba mata akan irin ayyukanta na kula da harkokin zamantakewar ma’aurata da ma al’umma baki daya don ganin anbi tsari da tarbiyyar addinin musulunci.

Aliyu Ibrahim ya kuma bada tabbacin daukar dukkan matakan da suka da ce don cigaban harkokin addinin musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *