• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mutanen Kano Na Murnar Kwashe Sharar Da Gwamnatin Kano Ta Yi

ByGlobal Tracker

Feb 16, 2023

Al’ummar unguwar magashi da ke yankin karamar hukumar Gwale sun bayyana farin cikin su bisa yadda gwamnatin jihar Kano ta ke aikin kwashe tilin shara mai matukar yawa da ta dami al’ummar yankin na tsawon lokaci.

Daya daga cikin shugabannin al’ummar yankin Malam Auwalu Ibrahim Magashi ne ya bayyana hakan lokacin da kwamitin koli na tsaftar muhalli na jihar Kano karkashin jagorancin kwamishinan muhalli na jiha Dakta Kabiru Ibrahim Getso suka kai ziyarar duba yadda aikin yake gudana.

Auwalu Magashi wanda yayi jawabi a madadin al’ummar yankin ya yabawa gwamnatin jihar Kano da kwamishinan muhalli bisa yadda suka jajirce wajen ganin an kwashe sharar wacce ta damu al’ummar yankin na tsawon lokaci.

Ku karanta: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano

Cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai da wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli ta jihar Kano Isma’il Garba Gwammaja ya sanyawa hanu ta Ambato Auwalu Ibrahim Magashin a cewa sharar ta dade tana kawo tsaiko a sha’anin sufuri a yankin.

Da yake jawabi, kwamishinan ma’aikatar Dakta Kabiru Getso ya ce bayan samun rahoton sharar tuni maaikatar ta tura jami’anta domin bibiya wanda ba’a dauki wani lokaci ba aka fara kwashe ta.

Ku Karanta: Yanzu–Yanzu: Wellcare Ya Nemi Afuwar Gwamnatin Kano Bayan Rufe Shi.

Kabiru Getso ya kuma bukaci al’umma da su rika kaiwa maaikatar rahoton duk wata shara ko matsalar muhalli da ta wuce musu gaba domin daukar matakin da ya da ce.

Kwamishinan ya kuma bukaci al’umma da su guji zubar da shara ba bisa ka’ida ba ko a magudanan ruwa da nufin kula da lafiyar al’umma, inda ya bayyana farin cikinsa ga al’ummar ta magashi bisa yadda suka yabawa gwamnatin Ganduje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *