Shugaban hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta a ta kasa a Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu ya ce Masu yi wa ƙasa hidima ne kadai za su yi amfani da na’aurar tantance masu kaɗa ƙuri’a ta BVAS a ranar zaɓe.
Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci cibiyoyin da ake bayar da horo ga ma’aikatan wucin-gadi da hukumar ta ɗauka dan gudanar da aikin zaɓen a babban birnin tarayyar Nigeria, Abuja.
Ya ce domin samun nasarar gudanar da zaɓen hukumar na buƙatar haɗin kan masu yi wa ƙasa hidima.
Haka kuma shugaban hukumar ya yi kira ga masu yi wa ƙasa hidimar da su zama masu biyayya ga Najeriya da ‘yan Najeriya ba jam’iyu ko wani ɗan takara ba.
Ya sake jajjada musu cewa kada su yadda su bayar da na’uara BVAS ɗin ga wani jami’in zaɓen, yana mai cewa za a riƙa bibiyar kowane ɗaya daga cikinsu.
Ku karanta: Ko A Dena Kashe Mutane A Gangamin Yakin Neman Zabe Ko Mu Hana Zaben — IPAC
Mahmoud Yakubu ya ce “Najeriya ta yi sa’a da ta samu ‘yan ƙasa irinku.
Babu yadda za a yi INEC ta gudanar da zaɓe ba tare da masu yi wa ƙasa hidima ba, kun zama dole sai da ku ake gudanar da zaɓen Najeriya. ba za mu iya gudanar da zaɓe ba tare da taimakonku ba.”
“Dan haka mun dogara a gareku da sauran ma’aikata.Kuma ku ne za ku yi amfani da abu mafi muhimmanci (BVAS) a harkar gudanar da zaɓen a kowacce rumfar zaɓe, inda kowanne mutum zai je domin kaɗa ƙuri’arsa. saboda haka kowanne daga cikinku zai rantse cewa zai zama ɗan ba-ruwanmu a zaɓen.