Kungiyar tarayyar kasashen Afirka (AU) ta ce dakatarwar da ta Yiwa Kasashe Uku da sukayi juyin a nahiyar Afirka tana nan Daram.
Kungiyar ta kuma sake nanata kudurinta na cewa ba za ta lamunci yin katsalandan ga dimokuraɗiyya da kuma sauya gwamnatoci da ke mulki a wasu ƙasashe a nahiyar ta hanyar yin juyin mulki ba.
A rana ta ƙarshe ta taron yini biyu da AU ta yi a Addis Ababa, ta ce dakatarwan da ta yi wa ƙasashen Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma Sudan yana nan daram – wanda ƙasashe ne da sojoji ke rike da iko bayan yin juyin mulki.
Kwamishinan harkokin siyasa na kungiyar, Bankole Adeoye, ya ce kungiyar a shirye take domin taimaka wa ƙasashen koma wa kan tsari na mulkin dimokuraɗiyya.
Shugabanni da suka halarci taron ciki harda shugaban Nigeria Muhammadu Buhari, sun kuma amince da batun tsarin kasuwanci maras shinge wanda ya kunshi dukkan ƙasashe a nahiyar ta Afirka.