• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Yi Babban Rashi a NNPP — Kabiru Rurum

ByGlobal Tracker

Feb 20, 2023

Dan majalisar tarayya Mai wakiltar Kananan Hukumomin Rano da Kibiya da kuma Bunkure a majalisar wakilai ta tarayyar Nigeria ya Mika Sakon ta’aziyyar sa ga iyalai da Yan uwa harma da Al’ummar Karamar hukumar Wudil bisa rasuwar Dan takarar majalisar wakilai ta tarayya Honarabil Kamilu Ado Isa.

Kafin rasuwar sa Kamilu Ado dai yana takara ne a karkashin tutar jam’iyar NNPP da zai wakilci Kananan Hukumomin Wudil da Garko a majalisar.

Cikin wata sanarwa da Mai taimakawa Rurum na Musamman a harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Fatihu Yusuf Bichi ya sanyawa Hanu wanda Global Tracker ta gani, ya bayyana rasuwar Dan takarar a matsayin Babban rashi ga mutanen Wudil da Garko da Kano ta Kudu dama jihar Kano baki daya.

Ku Karanta: Mutanen Kano Na Murnar Kwashe Sharar Da Gwamnatin Kano Ta Yi

Kabiru Alhassan Rurum yayi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya kuma sa Aljanna Firdausi ce makoma.

“Innalillahi wa Inna ilairrajiun, Amadadin shi kansa da iyalansa da mutanen kananan hukumomin Rano, Kibiya da Bunkure da Kuma daukacin Masoya da magoya bayansa, Maigirma Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum, Turakin Rano na Mika sakon ta’aziyya ga Injiniya Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da Injiniya Abba Kabir Yusuf da Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano Hon Umar Haruna Doguwa da Kuma daukacin Al’ummar karamar hukumar Wudil bisa rasuwar Dan takarar kujerar Majalisar wakilai ta kasa na yankin karkashin tutar Jam’iyyar NNPP Hon Kamilu Ado Isa.”

“Rt Hon Kabiru Alhassan Rurum na Addu’ar Allah ya jikan mamamcin ya gafarta masa yasa jannatul Firdausi ta zam Makoma gareshi.”

Rahotonni sun bayyana Kamilu ado dai ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya da ke da alaka da Numfashi na kusan kwanaki 14.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *