Gwamnatin jihar kano ta musanta zargin da wata kafar yada labarai ta yi cewa wata Mai dauke da juna biyu Shema’u Sani ta rasu a asibitin Koyarwa na Nassarawa saboda matsalar kin karbar tsohon kudi.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya sanar da haka yayin taron manema labarai Dangane da rasuwar Shema’u Sani Labaran yayin haihuwa a asibitin Nassarawa a makon da ya gabata.
Ya ce tun bayan fitar wancan labari, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano hadin guiwa da hukumar kula da manyan asibitoci ta jiha suka kafa kwamiti domin bincika lamarin.
Dakta Tsanyawa ya ce binciken da ma’aikatar lafiya ta gudanar ya gani cewa marigayiya Shema’u Sani Labaran an kai ta asibitin bayan ta dauki tsawon sa’o’i 4 tana zubar da jini a gida kafin a kawo ta asibitin, kuma tun bayan kawo ta asibitin Likitoci da sauran ma’aikatan lafiya suka duku fa domin ceto rayuwarta.
“Tun bayan karbar marigayiya Shema’u ba a saurari komai game da biyan kudi ba, ciki Kuma har da Kara mata jini”. Dr. Tsanyawa.
Ku Karanta: Masarautar Gaya Jigo ce a Cigaban Al’umma – Ibn-sina
Kwamishinan ya ce tun bayan umarnin gwamnatin jihar Kano na kula wa da mata masu dauke da juna biyu kyauta a dukkanin asibitin gwamnati babu wata alakar rasuwar Shema’u Sani Labaran da matsalar dena karbar tsohon kudi.
Idan za’a tunawa a makon da ya gabata ne wani mai suna Malam Bello ya yi hira da wata kafar yada labarai bisa zargin rasuwar Mai dakinsa Shema’u Sani asibitin Nassarawa saboda matsalar sabbin kudi.