• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

YANZU YANZU: Hadakar Kungiyoyin Matasan PDP Sun Koma APC a Kano

ByGlobal Tracker

Feb 20, 2023

Kungiyar Matasan jam’iyar PDP a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Nigeria sun sauya sheka daga jam’iyar PDP Mai hamayya zuwa jam’iyar APC Mai mulkin Kano da Nigeria Baki daya.

Shugaban gamayyar Kungiyoyin Kwamared Sani Shu’aibu Mai-Kwanika ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Kano.

Ya ce sun bar jam’iyar su ta PDP ne samakon rikice-rikice na ciki gida da yakai ga rashin sanin wanene takamaimai Dan takarar gwamna a jam’iyar da kuma wasu shara’o’i da har yanzu suke gaban kotuna daban-daban a nan Kano.

Ya ce dukkanin matsalin da jam’iyar ke fuskanta har zuwa yanzu da ya rage saura kwanaki 6 zaben shugaban kasa, amma dattawan jam’iyar sun kasa kawo masalaha dangane domin warware rikice-rikicen cikin gida da ya dame su.

Kwamared Mai-kwanika ya ce daga cikin dalilan da yasa suka ga dacewar komawa APC maimakon wata jam’iyar baya rasa nasaba da kokarin Gwamnatin Ganduje na daukar matakan tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ku Karanta: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano

Ya cigaba da cewa Gwamnatin APC Mai ci a yanzu ta Samar da ayyukan raya kasa da kuma tsayar da Dantakarar gwamna Wanda ya ke inganci da kuma zaman lafiya da al’umma wato Dakta Nasiru Yusuf Gawuna.

“Sakomakon bayan taro na masu ruwa da tsaki na kungiyoyyin matasa na jam’iyar PDP ta Kano State a kanan hukumomi (44).”

“Gida ya amince da barin jam’iyar PDP sakamakon riki ta-riki ta da takici taki
cin yewa da rashin ingattaccen shugabanci na jam’iyar da dattawa, da kuma matsalolin zaben cikin gida na yan takkarkaru musamman dan takarar gwamna da har yanzu bamu da cikakken dan takarar gwamna, hakan yasa
gida ya duba yaga duk a jam’iyyun nan babu wanda ya dace mu marawa baya
kamar jam’iyar APC saboda dalilai kamar haka:-

1. An samu kwanciyar hankali da tsaro a tsawon shekara takwas.

2. Anyi aikace aikacen raya kasa na mayar da birnin kano sabon birni.

3. Da kuma cikakkiyar demokaradiyya ta cikin gida.

Ku Karanta: Mutanen Kano Na Murnar Kwashe Sharar Da Gwamnatin Kano Ta Yi

4. Dan takarra gwamna kwararre ne kuma cikakken dan siyasa da tundaga 1999 ko wane gwamna yayi aiki dashi har yanzu wannan dama wasu dalilan ne yasa wannan kungiya ta umarci coordinators
na 44 LG, da kowa ya koma karamar hukumarsa, mazabarsa dama akwatinsa
domin tabbatar da nasarar jam’iyar APC, a kowanne mataki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *