• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

ZABE: Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro

ByGlobal Tracker

Feb 22, 2023

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro ta ƙasa a babban birnin tarayyaar Najeriya Abuja a yau Laraba.

BBC Hausa ta rawaito cewa an tattauna kan batutuwa da dama musamman ma kan tsari na tsaro da hukumomin tsaro suka yi gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

A lokacin da yake tattaunawa manema labarai bayan taron, sufeton ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya ce sun shirya tsaf domin gudanar da zaɓen da ke tafe.

Ya ce sun tanadi matakan tsaro da dama domin ƙare lafiyar waɗanda za su kaɗa kuri’a, inda ya buƙace su da su fito ba tare wata fargaba ba domin zaɓar wanda suke so.

KU KARANTA: YANZU-YANZU: Buhari ya Rantsar da Kwamitin Miƙa Mulki

Ya ce sun kuma faɗa wa shugaban ƙasa cewa yanayin tsaro na kyautata a Najeriya.

Shi ma da yake magana bayan kammala taron majalisar tsaron, ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya , Abubakar Malami, ya ce abin da ya sa gwamnatin tarayya ta kira taron shi ne domin ji daga hafsoshin tsaron ƙasar da shugabannin sauran hukumomin tsaro kan irin shirin da suka yi gabanin zaɓe da ke tafe.

Ya ce bayan ji daga garesu, gwamnati ta yi na’am da irin shirye-shiryensu, inda ya ce gwamnatin ta tanadi duk abin da ya kamata wajen ganin a samu nasarar gudanar da zaɓukan lami lafiya.

Manyan jami’an gwamnati da dama ne suka halarci taron

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *