• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Mun Saukar Alkur’ani Sau 200 Don Samun Shugabanni Na Gari — Balarabe Tatari

ByGlobal Tracker

Feb 23, 2023

Daga: Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar dake kula da gidaje da gine ginen kasuwar kantin kwari, ta gudanar da saukar karatun Alkur’ani mai-girma domin neman samun shugabanni nagari da samun saukin al’amura bisa halin matsin rayuwa da alummar Najeriya suke ciki a halin yanzu.

Shugaban kungiyar Alhaji Balarabe Tatari ya ce akwai gidaje sama da 160. da shugabancinsu dake kasuwar suka sauke kur’ani kamar yadda uwar kungiyar ta bukata Wanda ya gudana a fadin kasuwar baki daya a yau.

Tatari ya bayyana cewa, an gudanar da saukar ne domin Neman gafara ga Allah subahanahu wata’ala bisa kurakuran da alumma suka aikata da kuma neman taimakon Allah ya ba mu shugabanni nagari da samun bunkasar harkokin kasuwancin jihar Kano da ci gaban tattalin arzikin Najeriya.

KU KARANTA: Dausayin Larabci da Darussan Musulunci Ta Bukaci Tallafin Gwamnatoci Da Al’umma Don Samun Gurin Zama Na Din-Din-Din

Balarabe tatari, ya ce malamai da dama da yan kasuwa ne suka halarci saukar, wanda an sauke alkur’ani mai-girma da ya kai sau Dari biyu (200) dukka domin nemawa kasa da alummar Najeriya sauki.

Ya kuma yi kira ga sauran kungiyoyin yan kasuwa na ko ina a fadin kasar nan, da su koyi da irin tsari da kungiyar kula da gidaje da gine ginen kasuwar kantin kwari ta gudanar inda ya ce rashin aiwatar da irin wannan ba karamar Matsala bace ba ga alummar Najeriya, shiya ake ta shiga matsaloli da yawa.

Shugaban ya ce ya kamata alummar Najeriya su koma ga Allah ta hanyar kaucewa saba masa da dogaro a gareshi ba wai wani shugaba ba.

Daga nan shugaban kungiyar ya yabawa alummar da suka halarci Saukar da wadanda suka ba da gudunmawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *