Sanata Mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa ta kasar Nigeria Kabiru Ibrahim Gaya ya taya Honarabil Suleiman Abdurraham Kawu Sumaila Murna lashe zabe bayan da ya kayar da shi a zaben da aka gudanar a ranar asabar din da ta gabata.
Cikin wata nadaddiyar Muryar da GLOBAL TRACKER ta gani, Kabiru Gaya ya taya abokin takarar ta sa murna inda ya ce bashi da niyar Kai Kara kotu domin kalubalartar sakamakon zaben.
“Ina gaya masa cewa na ci zabe sai uku, kuma sau daya aka taba kaini kara, saboda haka nima bani da niyar kai shi kara kotu”, inji Kabiru Gaya.
Akwai Karin bayani….