Shugaban kasar Niger Mohamed Bazoum ya taya sabon zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu murnar cin zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.
Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Bazoum Mohamed ya ce yana taya ‘yan Najeriya murna bisa wannan nasara da kuma jajircewarsu na tabbatar da ci gaban dimokuraɗiyya.
Ya ce nasarar ba ta Najeriya kaɗai ba, nasara ce ga illahirin nahiyar Afirka.