Jam’iyyar Adawa ta Labour Party (LP) a zaɓen shugaban ƙasa na Najeriya ta bayyana cewa za ta ƙalubalanci sakamakon zaɓen da ya bayyana Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.
Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar LP, Datti Baba Ahmed ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai, ya na mai jaddada cewa akwai kura-kurai a zaɓen.
“Mun shiga zaɓen a matsayin LP kuma mun yi nasara da sunan LP,” a cewarsa. “Kuma za mu ƙwaci haƙƙinmu da sunan LP”.
KU KARANTA: Babu Dalilin Soke Zaben Shugaban Kasa — APC
Tun a ranar Talata jam’iyyun adawa na PDP da LP da ADC suka yi watsi da sakamakon a wani taron haɗin gwiwa, suna masu cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasar INEC ta gaza saka sakamakon a rumubun IReV da zai sa a gan shi ta shafin hukumar na intanet.
Peter Obi na LP ne ya zo na uku a zaɓen da ƙuri’u 4,223,277, inda Atiku Abubakar na PDP kuma yake biye wa Tinubu da ƙuri’u 6,301,741.