• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An sace Ma’aikatan kungiyar Red Cross a Mali.

ByGlobal Tracker

Mar 5, 2023

Kungiyar Bada agaji ta kasa da kasa wato Red Cross ta ce an sace Ma’aikatan ta a arewacin kasar Mali.

Kungiyar ta ce an sace ma’aikatan ne a tsakanin hanyar birnin Gao da Kidal da ke arewacin kasar, wanda yanki ne da ke fama da rikicin masu ikirarin jihadi na (IS).

Tun shekarar 2012, Mali ke fama da matsalar tsaro, sannan kuma sace sacen mutane don neman kudin fansa da kuma mayarwar gwamnati da kuma kama dai-dai kun a matsayin martani ya zamo ruwan dare a kasar.

KU KARANTA: Dakatarwar Da Muka Yiwa Kasashe Hudu Na Nan Daram — AU

Rikicin kasar dai ya fantsama zuwa makwabtanta kamar Burkina Faso da kuma Nijar, inda aka kashe dubban mutane da kuma raba wasu da dama da muhallansu.

Tashin hankalin ne dai ya janyo juyin mulkin da yayi sanadiyar Kofar da Gwamnatin tsohon shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita a shekarar 2020.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *