DAGA: IBRAHIM SANI GAMA
Sakataran kungiyar kasuwar Abinci ta Duniya dake Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi, ya sha alwashin ci gaba da baiwa Dakta Nasuru Yusuf Gawuna cikakken goyan bayan da ya dace domin ganin ya samu damar lashe zaben Gwamnan jihar Kano da sauran yan takara na jam’iyar APC a takarar majalisar dokokin jihar Kano.
Kwamared Rabiu Abubakar Tumfafi, ya ce sakamakon kyakyawan hali da mu’amulla da Dakta Nasiru Gawuna yake da ita ya sanya yake ta tashi fadi da karfinsa da Dukiyarsa da ilahirin alummarsa suke fafutuka domin ganin jamiyyar APC sun samu Nasara a zaben dake tafe ranar 11 ga watan nan da muke ciki.
Abubakar Tumfafi ya ce yanzu lokaci yayi da ya kamata alummar jihar Kano su mayar da alkairi da alkairi dangane da irin gudunmawar da Gawuna yake bayarwa a fadin jihar Kano da ma kasa baki daya.
KU KARANTA: Babu Dalilin Soke Zaben Shugaban Kasa — APC
Tumfafi yace yana kira ga matasa maza da mata da su fito kwansu da kwarkwata a ranar Asabar domin zubawa Dr Nasuru Yusuf Gawuna ruwan kuri,u domin samun damar ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma, bijiro da wasu sabbi, musamman ta fannin bunkasa harkokin kasuwanci da farfado da tattalin arziki da samarwa matasa ayyukan yi da ba da ilimi da sauran al’amuran raya kasa.
“Na dade yana hidimtawa jamiyyar APC tun daga kasa har zuwa jiha, musamman, wajen zuba Dukiyarsa domin kare mutuncin jamiyyar APC da Gawuna, tun yana shugaban karamar hukumar Nassarawa zuwa kwamishina har ya zama mataimakin Gwamnan Kano, wanda ga shi zai zama Gwamnan Kano da yardar Allah subahanahu wata’ala”, inji Tumfafi.
KU KARANTA: YANZU YANZU: Hadakar Kungiyoyin Matasan PDP Sun Koma APC a Kano
Haka kuma yanzu haka kwamared Tumfafi, yana ta kiraye kiraye a gidajen rediyo da kafafen sadarwa domin ganin an zabi Gwanin sa.
Daga nan yayi kira ga Yan jamiyyar APC da sauran alummar jihar Kano da yi duk maiyiyuwa wajen fitowa ranar zaben Gwamna domin zabar Dr. Nasuru Yusuf Gawuna da sauran yan takarar jamiyyar APC domin samun damar gudanar da ayyukan ci gaba da raya kasa da zarar sun lashe zabe.