• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Ku Kaucewa Shiga Bangar Siyasa Don Tsira Da Mutunci — Mustapha Abubakar

ByGlobal Tracker

Mar 9, 2023

BY: IBRAHIM SANI GAMA, KANO

 

Shugabancin kungiyar matasan yan kasuwar unguwar Gama Gidan kara ya shawarci matasan jihar Kano, musamman na yankin gama da su kaucewa shiga bangar siyasa a Musamman a lokacin da ma bayan zabe.

Shugaban matasan yan kasuwar Alhaji Mustapha Abubakar ne ya bukaci hakan a zantawarsa da manema labarai a Kano dake Arewa maso yammacin Nigeria.

Ya ce, lokaci ya yi da matasa ya kamata su yi karatun ta nutsu wajen kaucewa duk abin da zai haifar da fitina cikin alumma da kin yarda a yi amfani da su domin tayar da rigima ko wasu abubuwa da za su kawo tsaiko a tafiyar da alamuran siyasa.

Mustapha Abubakar, ya kuma yi kira ga matasa da su kaucewa shan muggun kwayoyi da sauran kayayyakin maye da yawo da makamai da za su kai ga illata lafiyar alumma ko furgitasu.

KU KARANTA: Bawa Mata Manyan Mukamai a Siyasa Zai Kawo Cigaban al’umma — San Kano

Shugaban ya kuma ce ta fannin kasuwanci a kasar nan, ya zama koma baya mutika wanda ya janyo lalacewar al’amura da tabarbarewar tattalin arzikin, wanda ana bukatar yin duba na tsanaki domin farfado da harkokin kasuwanci.

Shugaban ya bukaci Gwamanatoci a matakai daban daban, da su kasance masu sanya yan kasuwa a cikin tsarin kasuwanci da suka bijiro da shi domin bunkasar harkakin kasuwanci, maimakon dakko mutanen da basu San kasuwanci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *