• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Xi Jinping na China Zai ci Gaba da Mulki a Wa’adi na 3

ByGlobal Tracker

Mar 10, 2023

Shugaban kasar China Xi Jinping ya samu damar ci gaba da mulki a wa’adi na 3 a Juma’ar nan, abin da ya sa ya zama shugaba mafi karfin iko a kasar a cikin tsara da kakanni.

Nadin da majalisar dokokin kasar ta wa Xi na zuwa ne bayan da ya samu karin wani wa’adi na shekaru 5 a matsayin shugaban jam’iyyar kwaminisanci a watan Oktoban shekarar da ta gabata.

A wannan Juma’a, wakilan jam’iyyar suka zabe shi don yin wa’adi na 3, suka kuma sake nada shi a matsayin babban kwamandan rundunar sojin kasar.

KU KARANTA: Dakatarwar Da Muka Yiwa Kasashe Hudu Na Nan Daram — AU

An kawata dandalin Tiananmen da darduma ta kawa, da kuma allunan da ke nuna zabe mai mahimmanci da aka wa shugaba Xi, ga kuma makadan rundunar sojin kasar suna nishadantar da mahalarta dandalin.

Biyo bayan sanarwar sake bai wa Xi wa’adi na 3, wakilan jam’iyyar kwaminisanci sun sha rantsuwar nuna mubayi’a tare da kare kundin tsarin mulkin China.

Shafin intanet na RFI Hausa ya rawaito cewa jim kadan bayan haka ne shugaba Xi ya sha rantsuwar kama aiki, daga nan ya sha alwashin ci gaba da gina China tare da karfafa tsarin tafiyar da al’amuranta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *