• Wed. Jun 18th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Kamfanonin Aikin Hajji, Umara Na Fuskantar Karancin Kudi — Faisal Sani

ByGlobal Tracker

Mar 17, 2023

DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO

Shugaban kamfanin alkorash travel Agency ya koka dangane da yadda masu sana’ar hada hadar fitar da miniyyata aikin hajji da umara suke fuskatar kalubale saboda rashin kudaden takardun naira a hannun alummar Najeriya.

Shugaban kamfanin, Alhaji Faisal Sani ne yayi wannan kokawar a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dangane da halin da al’ummar Najeriya suka samu kansu a ciki na matsin rayuwa.

Faisal sani ya ce ya kamata Gwamnatin Najeriya da sauran masu fada a ji da su dauki matakan da suka da ce domin Neman hanyoyin da za’a samar da isassun takardun naira, kasacewar har yanzu mutane suna fama da karancin takardun naira a hannunsu.

KU KARANTA: Za Mu Zabi Gawuna Don Zama Gwamnan Kano — Rabi’u Tumfafi

Ya ce, duk da kotu ta ba da umarnin cewa a ci gaba da hada hada da tsofaffin kudaden naira, amma har yanzu bata sauya zani ba,domin kuwa mutane da dama suna kwana da yunwa da rashin kudaden ma da za su sayi ko ruwa da za su,inda yace wannan ba karamin kalubale bane ga Gwamnati da ma alummar Najeriya baki daya.

Shugaban kamfanin ya ce, yanzu mutane da suke zuwa umarah suna mutukar koka musu saboda matsalolin rashin kudaden takardun naira da suke fama da shi, su Kansu ajojin da suke sana’ar kai mutane suna fama da wannan yanayi da ake ciki a halin yanzu.

Alhaji Faisal Sani ya shawarci gwamnatin Najeriya da Babban bankin kasa akan ya yi iya kokarinsa domin buga sabbin takardun kudaden naira isassu domin a samu saukin al,amura yadda suka kamata,musamman duba lokacin hajjin bana ke karatowa, wanda yin hakan zai Samar da saukin alamuran yau da kullum.

Ya ce matasan kasar nan, suna fama da karancin ayyukan yi Wanda hakan na daya daga cikin abubuwan da suke har da matsalolin shaye shayen muggun kwayoyi shiga bangar siyasa ba gaira ba dalili,wannan na gurbata rayuwar matasa.

KU KARANTA: Muna Rokon Al’umma Su Guji Ta Da Hankali a Lokacin Zabe — Sarkin Kano

Shugaban kamfanin ya yi kira ga matasa da su kasance masu Neman na Kansu ta hanyar yin sana,oin dogaro da kai musamman yin kananan sana,oi ba wai sai ayyukan Gwamnati ba,koda ma sun yi karatu,karsu zauna domin jiran sai Gwamnati ta basu aiki.

Daga karshe ya ce kamfanin Alkuresh Travel and Agency, ya ce a koda yaushe yana yin abubuwan da za su dadadawa abokanan mu’amullar sa, musamma wajen yi musu aiki cikin kwanciyar hankali da lumana,shi yasa mutane da yawa suke son yin Hulda shi,musamman a wannan lokacin ummarah da hajji dake tafe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *