DAGA: ABDULMAJID HABIB ISA TUKUNTAWA, KANO
Tashin hankali baya haifar da da mai ido, sai kawo koma baya ga al’umma da sanadiyar rasa rayukan al’umma wanda hakan bai da ce ba a kowacce al’umma ko gari yankuna ko jihohi harma da kasa baki daya.
Bayanin hakan na cikin jan hankalin da mai unguwar Tukuntawa a karamar Kumbotso dake jihar Kano a arewa maso yammacin Nigeria Alhaji Nuhu Garba Musa Dan-Atumana yayi lokacin da yake jan hankalin al’ummar yankin dangane da muhimmancin zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dan-Atumana ya kuma yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka kasance tsintsiya da madaurin ki daya a zabukan shugaban kasa da aka gudamar a makonni uku da suka gabata, inda ya bukaci mutane dasu cigaba da zaman lafiya tare kuma da kada kuri’arsu cikin kwanciyar hankali a zaben gwamna da za’ayi a gobe Asabar a fadin tarayyar Nigeria.
KU KARANTA: Muna Rokon Al’umma Su Guji Ta Da Hankali a Lokacin Zabe — Sarkin Kano
Nuhu Dan-Atumana ya kara da cewa yankin ya kasance mai zaman lafiya a koda yaushe, a don haka akwai bukatar mutane su cigaba da daukar matakan da suka dace da nufin samin dauwwamammiyar zaman lafiya a yankin.
Cikin wata sanarwa da ya aikowa GLOBAL TRACKER ya ce “An yabawa kokarin jagororin jam’iyun siyasu na unguwar Tukuntawa, kan jarumta da dattaku da suka nuna wajen tabbatar da ganin an gudanar da zabukan da suka gabata cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, a fadin unguwar.”