DAGA: NAZIFI BALA DUKAWA, KANO
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke mutane 161 dauke da makamai, wadanda ake zargi da yunkurin kawo hautsini a lokutan da ake tsaka da gudanar zabukan gwamna dana ‘yan majalisun dokoki a sassa daban daban na jihar Kano.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano mai kula da harkokin zabe, Muhammed Hussaini Gumel, wanda ya fadi hakan lokacin da yake wa manema labarai jawabi yayin holen mutanen da jami’ansu suka kama a shelkwatar ‘yan sandan Kano dake Bompai ya bayyana cewa babu wani shafaffe da mai da ya fi karfin idan ya aikata ba dai dai ba rundunar ta kama shi.
Cikin wadanda rundunar ‘yan sandan jihar Kanon ta kama sun hadar da shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano kuma tsohon shugaban majalisar Honarabil Isyaku Ali Danja bisa zargin Bada Umarnin Kona ofishin hukumar zabe a Karamar hukumar sa ta Gezawa.
Sauran mutanen daga cikin 161 sun hada da Manajan Darakta na hukumar zirga-zirga ta jihar Kano wato Md Kano Line, Bashir Nasiru Aliko Koki da sauran wasu mutane daban daban da ake zargi da yunkurin haifar da rudani a cikin jama’a.
KU KARANTA: Murtala Kadage na NNPP Ya Lashe Zaben Dan Majalisar Jiha na Garko
Hussaini Gumel, ya ci gaba da cewa a yanzu haka suna dakon sakamakon zabe kuma suna nan ko da yaushe cikin shirin kota kwana, inda yaja hankalin masu murna ko nuna jimamin faduwa zabe da suyi abinsu cikin nutsuwa, batare da daukar makami ba.