Sabon wakilin karamar hukumar Birnin Kano da kewaye a majalisar wakilai ta kasa kuma Jigo a Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano (Hon.) injiniya Sagir Ibrahim koki ya aike da sakon taya Murna ga Sabon Zababban Gwamnan Jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf.
Honarabil koki Cikin Sanarwa da ya fitar and ranar ta talata ta Hannun Nazifi Bala dukawa Hadiminsa na Musamman kan harkokin Yada Labarai ta yabawa Al’ummar Jihar Kano bisa tsayawa tsayin daka da suka yi suka zabi Abba Kabir Yusuf suka kuma yi ta Addu’a har sai da nasarar ta tabbata.
KU KARANTA: Murtala Kadage na NNPP Ya Lashe Zaben Dan Majalisar Jiha na Garko
Dan majalisar wanda kuma shine (hasken municipal) jagoran ilimi da matasa ya ce zabin Abba Gida Gida da Mutanen Kano sukayi zai samar da gagarumin sauyi a gwamnati da siyasar Jihar Kano domin “a cewar sa gwamnati ce za’ayi ta Al’umma wacce zata zama gatan talaka.
A cewar sa suna da yakinin sabon Gwamnan na Kano zai mayar da hankali sosai a fannin Inganta Ilimi da kula da lafiya da bunkasa harkokin Kasuwanci da Noma da sauran Abubuwan bunkasa rayuwar Al’umma.
Hon sagir koki yayi amfani da wannan dama wajen Mika sakon taya Murnar sa ga Madugun Darikar Kwankwasiyya Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma Sabon Gwamnan na Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a madadin iyalansa da ‘yan uwa da kuma daukacin Al’ummar mazabarsa ta Birni da kewaye.