• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Ga Watan Azumi a Nigeria — Sarkin Musulmi

ByGlobal Tracker

Mar 22, 2023

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar na uku ya sanar da ganin jaririn watan Ramadan na shekarar 2023 a wasu sassan Najeriya.

A jawabin da ya yi na sanarwar wanda aka sanya a shafin Facebook na kwamitin ganin watan, Sarkin Musulmin ya ce an ga watan ne bayan samun rahotanni daga shugabannin addinin Musulunci da ke wasu jihohin ƙasar.

KU KARANTA: LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda Magoya Bayan APC Suka Gudanar da Zanga-zangar Kin Amincewa da Sakamakon Zaben Gwamnan Kano

Hakan na nufin ranar Alhamis 23 ga watan Maris din 2023 ne za ta kasance daya ga watan Ramadan.

Rahotanni sun bayyana cewa an ga watan a garin makarfi na jihar Kaduna da garin Fataskun na jihar Yobe da ma wasu sannan kasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *