• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Tsaftar Muhalli: Kotun Tafi Da Gidan Ka Ta Ci Tarar Mutane 34

ByGlobal Tracker

Mar 25, 2023

Kotun tafi da gidan ka ta kwamitin Koli na tsaftar Muhalli na Jihar Kano ta Kama mutane 34 da lefin karya dokar tsaftar Muhalli da ake gudanarwa a duk asabar din karshen wata a jihar Kano dake Arewa maso yammacin Nigeria.

Kotun karkashin jagorancin majistire Auwal Yusuf Suleiman ta Sami mutanen 34 da lefin karya dokar inda aka yi musu tarar naira dubu 40.

Da yake tattauna da manema labarai Jin kadan bayan duba yadda aikin tsaftar Muhallin ya gudana a Kanon, kwamishinan Muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ja kunnen matuka baburan adaidaita sahu wanda su aka fi kawama da lefin da su guji karya dokar domin Gwamnatin Jihar Kano ba za ta zuba Ido a cigaba da aikata lefukan ba.

KU KARANTA: Za Mu Tabbatar Da Kwashe Dukkan Sharar Kofar Wambai — Getso

Ya ce Gwamnati a shirye take na daukar dukkan matakan da suka da ce domin rage ko kawo karshen aikata lefukan da suka danganci tsaftar Muhalli a fadin jihar.

Kwamishinan ya yabawa al’ummar jihar Kano bisa yadda suke bin dokar na zaman gida tare da tsaftace yankunan su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *