• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Yan Kasuwa a Ungogo Sun Ta Ya Abba K. Yusuf Murnar Lashe Zabe

ByGlobal Tracker

Mar 25, 2023

Kungiyar Dattawan yan kasuwar Singa na unguwar zango a karamar hukumar Ungogo a nan jihar Kano ta nuna mutukar farin cikinta bisa nasarar da Dan takarar jam’iyar NNPP Abba kabir Yusuf, ya samu a zaben Gwamnan jihar Kano.

Shugaban kungiyar Alhaji Sammani Mohammad Abdulmuminu, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar Singa.

Sammani ya taya Abba kabir Yusuf, murna da fatan alheri domin Nasarar da ya yi wanda a cewarsa ta samu ne sakamakon addu’o’i da suka rika yi tare da kokarin ganin mutane sun zabe shi.

Ya ce yanzu lokaci yayi da Gwamnatin Abba kabir Yusuf, za ta fara sauke alkawarin da ta dauka a yayin yakin Neman zaben Gwamna Dana yan majalisun dokoki musamman bangaren harkokin ilimi Wanda shine jigon kawacce alumma a cikin kwanakin Dari na farkon zangon mulkin Gwamna Abba kabir Yusuf.

Alhaji Sammani, ya ce yana da kwarin gwiwar gwamnatin Abba Gida_Gida za kuma ta yi duba a fannin harkokin kiwon lafiya da kasuwanci, musamman yadda jihar Kano ta ke cibiyar kasuwanci, ya na mai cewa ya kamata su samar da managartan tsare tsare da za su inganta rayuwar matasa da yan kasuwa.

KU KARANTA: Jigo a NNPP Sagir Koki, Ya Taya Abba Gida-gida Murnar Lashe Zabe

Ya ce hakan ba zai yi yu ba sai alummar jihar kano sun baiwa Gwamnatin cikakken goyan bayan daya kamata musamman addu,oin da za su taimaka wajen cimma nasarar da ake da bukata.

Sammani zango, ya sha alwashin cewa kungiyar a shirye suke wajen ci gaba da baiwa Abba kabir Yusuf, hadin kan daya kamata domin kawo babban ci gaba mai dorewa a kawanne fanni domin ganin alummar jihar Kano, sun amfana.

Haka zalika, ya shawarci matasa maza da mata da sauran yan kasuwa da su kwantar da hankulan su domin wannan Gwamnati ce da za ta taimaki alumma da bunkasa harkokin da suka durkushe, musamman lafiya da kasuwanci da ilimi da sufuri da tsaro da sauran al’amuran rayuwa.

Daga karshe ya yabawa alummar jihar Kano da suka fito suka kuma, jajirce da ba da gudunmawar da ta kamata domin kawo sauyin Gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *