Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya jaddda goyon bayansa bisa tsarin e-naira da babban bakin Nigeria CBN ya bujiro dashi zai taimaka wajen bunkasa harkokin Kasuwanci da cigaban kasa.
Mai Martaba Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar bakuncin daraktan CBN shiyar Kano Alhaji Muhd Hamisu Musa yayin da suka ziyarce shi a fadar sa.
Bayero ya ce tsarin na E-naira zai tamakawa yankasuwa da sauran al’ummar kasar nan.
Ya kuma bukaci da babban bakin kasa da ya gyara matsalar network da ake samu yayin hada-hadar kudade, wanda a cewar sarkin yana kawo Nakasu da tarin kalubale da al’umma ke fuskanta.
KU KARANTA: Muna Rokon Al’umma Su Guji Ta Da Hankali a Lokacin Zabe — Sarkin Kano
A nasa jawabin babban daraktan bankin Alhaji Muhd Hamisu Musa ya ce sun ziyarci fadar sarkin ne domin shaida masa irin hanyoyin da suke bi wajen wayar da kan alumma amfanin tsarin na E-naira da babban bakin kasa ya bujiro da shi domin taimakawa yan kasuwa.
A yayin ziyarar, daraktan na tare da dukkan shugabannin sassa na bankin shiyyar Kano.