• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

VIDEO: Yadda Shugaban Kamfanin “Dan-kata Investment” Ya Rabawa Mutane Kusan 2,000 Kayan Abinci

ByGlobal Tracker

Mar 31, 2023

DAGA: YAHAYA SADISU ALKASIM, KANO

 

Daya daga cikin Yan kasuwa a Kano dake Arewacin Nigeria Alhaji Abubakar Sadiq Dan Gaske ya bukaci al’umma da su rika tallafawa mabukata da masu karamin karfi musamman a wannan wata na ramadan don samun falala a gurin Allah.

Abubakar Sadiq Dan-Gaske ya bayyana hakan ne lokacin da yake raba kayan abinci da suka hadar da shinkafa da Taliya ga mutane sama da dubu 2 a nan Kano.

Ya ce yanayin da ake ciki na matsin rayuwa da kuma wahala samakon hauhawar farashin kayan masarufi ne ya ja hankalin sa yaga dacewar tallafawa marayu da marassa karfi da kuma sauran al’umma.

Abubakar Dan-Gaske ya bukaci sauran mawadata a nan Kano da su rika tallafawa masu karamin karfi domin hakan yana ragewa al’umma radadin da suke a ciki.

Wasu da suka amfana da tallafin sun bayyanawa wakilin GLOBAL TRACKER dadin da suka ji inda suka yi masa fatan alkhari a rayuwar da ma iyalinsa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *