Kasar Rasha ta karɓi shugabancin kwamitin taro na Majalisar Ɗinkin Duniya duk da ƙoƙarin makociyar Rashan wacce kuma suke yakar juna a yanzu wato Ukraine na ganin hakan bai tabbata ba.
Duka mambobin kwamitin 15 sukan jagoranci kwamitin tsawon wata guda a wani tsarin shugabancin kwamitin na karɓa-karɓa.
Rabon da Rasha ta jagoranci kwamitin tun a watan Fabrairun 2022, lokacin da ta ƙaddamar da ta fara yaki da kasar Ukraine.
Hakan na nufin a yanzu kwamitin tsaron na Majalisar Dinkin Duniya na ƙarƙashin jagorancin ƙasar da shugabanta ke fuskantar yiwuwar kamu kan zargin laifukan da suka shafi yaƙi.
KU KARANTA: Rasha ta Kama Dan Jaridar Amurka Bisa Zargin Leken Asiri
A watan jiya ne kotun hukunta manyan laifuka ta duniya wadda ba a ƙarƙashin Majalisar Dinkin Duniya take ba – ta ba da sammacin kama shugaban Rasha Vladimir Putin.
Duk da ƙorafin da Ukraine ta yi, Amurka ta ce ba za ta iya hana Rasha – wadda ke da kujerar dindindin a kwamitin tsaron – ɗarewa kan shugabancinsa ba.
Sauran ƙasashen da suke da kujerar dindindin a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun haɗar da Birtaniya da Amurka da Faransa da kuma China.
BBC Hausa