Daurarru sama da dubu daya ne dake zaune a gidajen gyaran hali na goron Dutse da Kurmawa a nan Kano suka amfana da ganin likitoci daban daban tare da ba su magani kyauta.
Yayin wani aikin sa kai da nufin neman lada a wajan Allah madaukakin sarki da tawagar kungiyar likitoci musulmi suka yi karkashin jagarancin shugaban kwanitin gudanar da aikin Dakta Sule Abdullahi Gaya.
Har ma shugaban kungiyar na jihar Kano Dakta Muhammad Auwal ya ce suna yin aikin ne dan taimakawa marasa karfi a wurare daban daban, tare da basu kayan abinci da ruwa, da makamantan su.
KU KARANTA: LABARI CIKIN HOTUNA: Gobara Ta Cinye Babban Asibiti a Bebeji
A jawaban su daban daban Dakta Anas Ibrahim Yahaya Bichi da Dakta Muhammad Lawan Adamu wadanda suna cikin likitocin da suka duba marasa lafiya da dama cewa suka yi a tafiyar ta su babu irin likitan da babu, dan haka kowacce irin cuta suka ci karo da ita sun tanadi maganin ta ko likitian da zai bawa marar lafiya magani.
Daga bisani mai kula da gidan gyaran halin na Kurmawa DC Mu’azu Tukur wanda ya yi jawabi a madadin shugaban hukumar ya nuna godiya da jin dadin su kan aikin da kungiyar likitoci musulmi suka yi ga daurarrun.