• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Ranakun Hutun Ester

ByGlobal Tracker

Apr 5, 2023

Gwamnatin Tarayyar ta bayyana ranakun Juma’a 7 ga watan Afrilu da kuma Litinin 10 ga wata a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan bikin Easter na wannan shakarar.

Ministan cikin gida na ƙasa Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma’aikatar Shuaib Belgore ya fitar ranar Laraba.

KU KARANTA: YANZU-YANZU: Buhari ya Rantsar da Kwamitin Miƙa Mulki

Sanarwar ta buƙaci kiristocin ƙasar da su yi koyi da halayen sadaukarwa, da haɗin kai, da yafiya, da mutunta juna, da soyayya da zaman lafiya da haƙuri na Yesu Almasihu.

Ministan ya kuma yi kira al’ummar Kiristocin ƙasar da su su yi amfani da lokutan bukukuwan na Easter domin yi wa ƙasar addu’o’in samun zaman lafiya da kawo ƙarshen matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *