• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Matuka Akori-kura Sun Roki Gwamnati Matsuguni Na Din-din-din

ByGlobal Tracker

Apr 5, 2023

DAGA: IBRAHIM SANI GAMA, KANO

 

Kungiyar matuka motocin Akori-kura ta kasa reshen jihar Kano dake railway, tana ci gaba da kokawa dangane da rashin guri na din-din-din da kungiyar take fama da shi duk da kudaden haraji da take Tarawa Gwamnati.

Shugaban kungiyar Abubakar Dan-iya Bala ne ya bayyana haka a lokacin da yake yiwa manema labarai Karin haske a ofishinsa dake nan Kano.

Shugaban ya ce kungiyar tana fuskantar kalubale saboda rashin wuraren tsayawa wanda ta sanya kungiyar ta ke kashe makudan kudade na haya Wanda da Gwamnatin ta Samar da guraren ita ce za ta amfana da irin wadan nan kudade.

Abubakar yayi fatan wannan sabuwar Gwamnati da za ta karbi ragamar mulki za ta kalli fannin harkokin sufuri domin kawo masa daukin gaggawa da zai tallafawa matuka motocin Akori-kura da sauran bangaren sufuri.

Shugaban ya kara da cewa Gwamnatin da za ta karbi mulki kamata yayi ta Samar da motocin sufuri ta hanyar baiwa kungiyoyin sufurin da suka San bangaren domin baiwa ya’yanta, kasancewar kungiyar ta San irin wadanda za’a baiwa matsayin tallafawa rayuwarsu da Samar musu da ayyukan yi domin dogaro da kai.

KU KARANTA: Tsarin e-Naira Zai Taimaka a Bunkasa Kasuwanci a Nigeria — Aminu Ado

Shugaban ya jaddada cewa, babu wani tagomashi ko tallafi da Gwamnati ta yiwa kungiyar duk da gudunmawar da suke baiwa Gwamnatoci a matakai daban daban.

Kungiyar kuma ta ya zababben Gwamanan Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf Murnar nasarar daya samu.

Dan-iya Bala ya shawarci yan kungiyar da su kasance masu bin dokokin da Gwamnati ta sanya musamman wajen mallakar takardun mota da dena Dorawa motaci kayan da suka wuce kima da gudun wuce sa’a da karya dokokin da suka shafi kan hanya.

Ya kuma bukaci yan kungiyar da su ci gaba da baiwa shugabanci hadin kai da goyan baya domin samun damar bijiro da managartan shirye shirye da su inganta rayuwar alumma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *