DAGA: ABDULMAJID HABIB ISA TUKUNTAWA, KANO
Mai martaba sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulkadir ya nada Mujahid Bello Idris a matsayin sabon dagacin garin Gumakka dake karamar hukumar Warawa.
Nadin nasa ya biyo bayan rasuwar Mahaifinsa tsohon dagacin garin na gumakkan Malam Bello idris.
Mai martaba sarkin ya hori sabon dagacin Akan rike amanar Al’umma da Kuma saurarensu Akoda yaushe.
Shima sabon dagacin garin gumakkan ya godewa Allah da ya nuna masa ranar da ya bayyana a matsayin ta tarihi a rayuwar sa da inda kuma yabawa Mai martaba sarkin na Gaya.
KU KARANTA: Ina Taya Kawu Sumaila Murna, Bazan Kai Kara Kotu Ba — Kabiru Gaya
Ya Kuma roki hadin kan Alummar da zai jagoranta tare da Addu’ar Allah ya jikan marigayi tsohon dagaci.
Shima a nasa ban garan, Mai unguwar Gumakkan Abubakar Haruna ya taya sabon dagacin murnar samun matsayin tare da Bada tabbacin yin duk Mai yuwuwa domin samun Nasarar da aka Sanya a gaba.