• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

YUMSUK: SUG Ta Roki Karin Adadin Sabbin Daliban Da Ake Duba Lafiyar Su

ByGlobal Tracker

Apr 5, 2023

Shugaban Kungiyar Daliban Jami’ar Yusuf Maimuna Sule (YUMSUK) dake Kano a Arewa maso yammacin Nigeria ya bukaci a kara adadin sabbin daliban da ake wa Gwajin lafiya.

Tafida Akilu wanda shine sabon shugaban kungiyar daliban (Student Union Government SUG) yayi rokon a Kara Adadin ne a Asibitin Jami’ar dake mazauninta na Din-din-din a Kabuga yayi tattaunawarsa da manema labarai.

“Wannann duba lafiyar ana yin sa ne ga dukkanin sababbin daliban da aka bawa gurbin karatu a jami’ar, domin tabbatar da cikakkiyar lafiya kafin fara karatu,” inji Akilu.

KU KARANTA: Ba Zan Yi Wa Sabon Gwamnan Kano Katsalandan Ba – Kwankwaso

A yayin ziyarar tasa, Tafida ya tattauna da likitocin da ke Duba Lafiyar Daliban a Jami’ar da nufin ko akwai wani kalubale da suke fuskanta wanda kungiyar zata iya Bada Gudun mowa domin shawo kan matsalar.

A karshe shugaban daliban yayi kira da sabbin daliban da su dena cinkushewa a can sashin na Kabuga da suke zuwa daya sashin dake kofar Nasarawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *