• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Banji Dadin Yadda Zakarana Ya hada Ni Fada Da Makocina Ba — Me Zakaran Da Aka Yankewa Hukunci Kisa

ByGlobal Tracker

Apr 8, 2023

Mutumin da ya mallaki zakaran da aka zartar wa hukuncin kisa a jihar Kano dake Arewacin Nigeria, ya ce bai ji daɗin yadda marigayin ya haɗa shi faɗa da maƙwabcinsa ba.

A ranar Talatar da ta gabata ne, Mai shari’a Halima Wali a wata kotu da ke Kano ta yanke wa zakaran hukuncin kisa

Matakin ya zo ne bayan wasu maƙwabtan mai zakaran biyu suka shigar da ƙara, inda suka zargi zakaran da hana su sakat saboda yawan cara, da zarar sanyin asuba ya kaɗa.

A tattaunawarsa da BBC, mai zakaran, Isiyaku Shu’aibu, mazaunin unguwar Ja’en a birnin Kano, ya ce bai taɓa samun saɓani da makwabcinsa ba a tsawon shekaru 20 sai a dalilin zakaran.

Ya kuma ce ba zai yi kewar zakaran ba, kasancewar ba wata shaƙuwar ƙut-da-ƙut suka yi ba.

Isyaku ya shaida wa Yan jaridu cewa yara ne ma suka yanka rigimammen zakaran kafin ma ya dawo gida a ranar Juma’a.

KU KARANTA: Tsaftar Muhalli: Kotun Tafi Da Gidan Ka Ta Ci Tarar Mutane 34

Tun farko, ɗaya daga cikin waɗanda suka shigar da ƙarar, Yusuf Muhammad, ya ce carar da zakaran ke yi, tana shiga haƙƙinsa don kuwa ba ya samun barci cikin lumana.

Isyaku Shu’aibu ya faɗa wa kotun cewa da ma ya sayi zakaran ne don bikin Easter, inda ya buƙaci kotun ta yi masa rangwame zuwa ranar Juma’a kafin zartas masa da hukunci don amfani da naman a ranar Good Friday, abin da kotun ta amince da shi.

Bayan rokon isiyakun ne kotun ta amince da bukatar tasa inda ta Bada Umarnin Yanka Zakaran a jiya jumaa.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *