• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Bashariyya Foundation Ta Yiwa Marayu 55 Kayan Sallah

ByGlobal Tracker

Apr 10, 2023

DAGA: KAMAL YAKUBU ALI, KANO

 

Gidauniyar tallafawa Marayu da masu Karamin karfi wato “Bashariyya foundation” dake unguwar yan-tandu a karamar hukumar Dala ta tallafawa marayu da kayan abinci da kayan sallah domin rage musu radadin halin maraici da suka tsinci kansu a ciki.

Shugaban kungiyar Malam Bashir Aliyu ya ce suna gudanarda da Rabon kayayyakin tallafin ne Shekaru hudu da suka gabata domin tallafawa marayun dake unguwanni Adakawa yan tandu domin ganin sun gudanar da Azimi da bukukuwan sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.

Ya ce marayu 55 ne suka Amfana da tallafin kayan sallah da Sabulun wanka da kuma kayan Abinci wanda Kungiyar ta raba musu domin rage musu radadi da kuma ganin ta taimakawa wadanda iyayen su suka rasu.

Ya ce tallafawa marayu yana daga cikin ayyukan da Allah yake farin ciki dashi hakan ne yasa kungiyar take zage damtse wajen ganin ta gudanar da Rabon kayayyakin ga Marayun dake yankin.

KU KARANTA: Muna Bawa Inganta Rayuwar Marayu Fifiko a Koda Yaushe — Sani Wakili

Wasu daga cikin Marayun da Suka amfana da tallafin Aisha Sabiu da Jibrin Yahya sun bayyan farin cikinsu  dan gane da tallafin da aka basu.

Taron ya gudana a farfajiyar makarantar dake unguwar yan-tandu dake yankin karamar hukumar Dala wanda ya samu halarta iyayen Marayu da kuma manayan unguwa da limamin masallacin Adakawa malam Nura Tahir da sauran alumma da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *