DAGA: IBRAHIM AMINU RIMIN-KEBE
Zababban dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Minjibir da ungogo, a jam’iyyar NNPP, Honarabil Sani Adamu Wakili ya jagoranci rabon kayan sallah ga marayu kimanin 320 a kananan hukumomin Minjibir da ungogo a jihar Kano.
Dan majalisar ya bayyana cewa, koda a shekarar data gabata sun dinkawa marayu kimanin 150 kaya tare da basu kyauta domin gudanar da bikin sallah kamar kowa.
Wakili, yana mai bayyana cewa, akwai bukatar wadata dake cikin al’umma dasu tashi tsaye wajen cigaba da tallafawa rayuwar marayu da kuma marasa karfi dake kusa dasu a wannan lokacin na matsin tattalin arziki.
A ranar asabar din data gabata ne Honarabil Sani Adamu Wakili ya jagoranci rabon kayan sallah ga marayun a karamar hukumar Minjibir wacce take da mazabu 11 wanda ya gudana a cikin garin minjibir taron daya samu halartar zababban dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar minjibir Honarabil A.A Minjibir.
KU KARANTA: VIDEO: Yadda Shugaban Kamfanin “Dan-kata Investment” Ya Rabawa Mutane Kusan 2,000 Kayan Abinci
Hakazalika a ranar lahadin data gabata rana ta karshe, Honarabil Wakili jagoranci rabon kayan sallah ga marayun a karamar hukumar ungogo mai mazabu 11 wanda ya gudana a cikin garin ungogo wanda Kuma ya samu halartar dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar ungogo a majalisar dokokin jihar Kano Honarabil Aminu Sa’adu Ungogo, Shugaban jam’iyyar NNPP na karamar hukumar ungogo Alhaji Bilyaminu Bachirawa da sauran manyan baki.

Dan majalisar tarayya, ya tabbatar da cewa zai mai mayar da hankali a fanin harkokin kiwon lafiya dakuma ilimi a kananan hukumomin guda biyu.
Ya Kara da cewa, akwai batun samarwa da matasa aiyukan wadanda zasu dogara da kan su dakuma baiwa mata jarin dasu dogara da kan su dan kaucewa zaman kashe wando.
Daga bisani zababban dan majalisar tarayyar, ya tabbatar da cewa zai bakin kokarin sa da zarar ya kama aiki domin samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar da yake wakilta.