• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Muna Roko A Daga Darajar Shafin Intanet na YUMSUK — Shugaban Dalibai

ByGlobal Tracker

Apr 12, 2023

DAGA: MUSTAPHA MUHAMMAD KANKAROFI

 

Shugaba daliban Jami’ar Yusuf Maitama Sule wato (YUMSUK) dake Kano a Arewa maso yammacin Nigeria Tafida Sabo Akilu yayi kira ga sashin kimiyya da fasaha na jami’ar da su gyara Shafin yanar gizo na makarantar domin daliban jami’ar su sumu damar biyan kudin makaranta a kan lokacin.

Tafida Yayi kiran ne yayi wata ziyara da ya kaiwa shugaban sashin dake kula da shafin yanar gizo a ofishin sa dake mazaunin jami’ar dake kofar Nasarrawa a Kano.

Ziyarar ta biyo bayan matsala da aka samu a shafin yanar gizo na jami’ar, inda dalibai ke shan wahala wajen biyan kudin makaranta.

Shima ana sa bangaren, shugaban sashin na kimiyya da fasaha na Yusuf Maitama Sule Farfesa Ishola Dada Muraina ya bada tabbacin cewa nan ba da jimawa ba komai zai daidaita domin ganin daliban sun samu damar biyan kudin na zangon karatu.

KU KARANTA: YUMSUK: SUG Ta Roki Karin Adadin Sabbin Daliban Da Ake Duba Lafiyar Su

Muraina ya Kuma bawa daliban hakuri dangane da matsalar da aka samu wanda yayi alkwarin magance cikin kankanin lokacin.

Sabon shugaban daliban yana kai wannan ziyarar ne domin samun kyakyawar alaka da hadin kai da shugabanin bangarori na jami’ar a wani salo na kawowa dalibai cigaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *