Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa INEC ta dakatar da kwamishinan zaɓe na jihar Adamawa, Barista Hudu Ari daga aiki.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, INEC ta umarci kwamishinan ya fice daga ofishinta har sai abin abin da hali ya yi.
Ta ce daga yanzu sakataren hukumar a jihar Adamawa ne zai karɓi ragamar aiki.
Hukumar ta ce an dakatar da kwamishinan zaɓen ne har sai an kammala bincike, inda daga nan ne INEC za ta bayyana matsayarta kan lamarin.
A ranar Lahadin da ta gabata ne kwamishinan zaɓen Adamawa ya fito ya sanar da Aisha Binani a matsayin wadda ta lashe zaɓen gwamnan jihar tun kafin a kammala tattara sakamako.
Sai dai INEC ta ce matakin da ya ɗauka haramtacce ne, don haka ba za a yi aiki da shi ba.
BBC Hausa