Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bayyana fadan da ya barke tsakanin sojojin gwamnati da rundunar masu sanye da kayan sarki ta RSF a Sudan da cewa abin damu wa ne matuka.
Buhari ya bayyana haka ne lokacin da shugaban gwamnatin mulkin soji na ƙasar Chadi, Janar Mahamat Idriss Déby ya kai masa ziyara a Makkah da ke Saudiyya.
Shugaban Najeriyar ya nuna takaici kan irin asarar rayuka da ake ci gaba da samu sakamakon rikicin.
Shugabannin biyu sun tattauna kan batun rikicin na Sudan, inda suka yi kira ga dukkan ƙasashe makwaɓta da kuma al’ummomin waje da su shiga tsakani domin dakatar da faɗan.
KU KARANTA: Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hakar Man Fetir a Nassarawa
“Lamarin da ke faruwa a Sudan abin takaici ne.
Sudan ta cancanci zaman lafiya idan aka duba halin da ta shiga a baya,” in ji Buhari.
Buhari ya kuma yaba wa shugaban na Chadi kan irin kokari da yake yi na ganin hankali ya kwanta a Sudan da kuma samun zaman lafiya.
Deby-Itno ya faɗa wa shugaba Buhari cewa abin da ke faruwa a Sudan abin damuwa ne wanda idan ba a ɗauki matakin shawo kan shi ba, zai iya yin mummunar tasiri kan ƙasashe makwaɓta.
Shugaban na Chadi ya ce cikin irin matakai da ƙasarsa ta ɗauka kan rikicin, sun haɗa rufe iyaƙar ƙasar da Sudan da ƙara karfafa matakan tsaro.
BBC Hausa