Daya daga cikin jagororin jam’iyar NNPP kuma Mai Neman takarar shugabancin Karamar hukumar Ungogo Shafi’u Hussain Bachirawa ya taya jagoran jam’iyar NNPP na kasa Injiniya Dakta Rabi’u Musa kwankwaso da zababban gwamnan Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf Murnar bukukuwan Karamar Sallah.
Shafi’u Bachira ya bayyana hakan ne a madadin iyalai da Yan uwa da kuma magoya baya a sakon sa na barka da Sallah ga shugabannin da kuma al’ummar jihar Kano.
Ya ce ya fara samar da tsare-tsaren da matukar ya yi nasarar zama shugaban Karamar hukumar Ungogo zasu tallafawa wajen bunkasa harkokin kasuwancin da tattalin arziki da Ilimi da lafiya da kuma samar da ayyukan yi ga Mutanen yankin.
KU KARANTA: Ba Zan Yi Wa Sabon Gwamnan Kano Katsalandan Ba – Kwankwaso
“Matukar Allah ya bamu dama zamu samar da ayyukan yi, kowa yasan Gwamnatin Injiniya Dakta Rabi’u Musa kwankwaso da akayi a baya ta samar da ayyuka ga Matasa, ta Kai Yara da manya makarantu a Nigeria da kasashen ketare, to muma zamu samar da tsare-tsaren da zasu tallafawa Rayuwar al’umma,” inji Bachirawa.
Bachirawa ya ce “Kasancewar mu a wannan yanki a irin mu’amalar da muke da mutane, mun tattauna da mutane da ire-iren bukatun da al’umma suke bujiro da shi, saboda haka zasu yi amfani da dukkan bayan da muke da shi da kuma Wanda al’umma zasu bujiro da shi domin aiwatarwa da nufin cigaban wadanda muke fatan wakilta.”
Daga nan ya bukaci al’ummar jihar Kano da su cigaba da ta ya zababban gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabiru Yusuf addu’o’in gudanar da ayyukan da zasu bunkasa rayuwar al’umma da kuma yaki da matsalolin da suke damun Mutanen Kano.