Alummar Unguwar Tunga dake karamar Hukumar Gwale a jihar Kano Sun Kai kokensu kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na Kano, Jigawa da Katsina KEDCO don nuna damuwarsu kan halin matsin da suka tsinci kansu sakamakon karancin hasken wutar lantarkin da suke fama da shi.
Da yake jawabi lokacin da alummar unguwar suka yi dandazo zuwa ofishin kamfanin KEDCO da ke unguwar chiranchi kan titin zuwa fanshekara, shugaban Ayarin Alhaji Ahmad Ango ya ce rashin samun hasken wutar lantarkin ya jefa alummar unguwar cikin halin kaka ni kayi.
Ya ce duk da cewa alummar unguwar na da himma wajen biyan kudin wuta, amma abin takaici shine yadda kamfanin na KEDCO ya mayar da unguwar ta Tunga saniyar ware a fannin ba da hasken wutar lantarki.
KU KARANTA: KANO: Mun Shirya Tsaf Don Nishadartar da Masu Bude Ido — Shugaban Hukumar Kula da Gandun Daji
“Da kyar ake bamu wutar minti 30 a cikin awa 24, bayan unguwannin da ke makwabtaka da mu irinsu janbulo, dorayi karama, unguwar Bello, kabuga kullum cikin samun hasken lantarki suke, me mutanen tunga suka yiwa KEDCO ne a basa samun wutar?” inji Malam Ahmad Ango.
Ya ce sunje ne da korafinmu a rubuce, kuma suna bukatar shugabancin kamfanin KEDCO mai Adalci ya shigo cikin batun don kawowa alummar Tunga doki.
Da take jawabi a madadin kamfanin KEDCO wata jami’ar kamfanin Hajiya Fauziya ta ce za su duba lamarin kuma za’a sami maslaha.