• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Majalisar Dinkin Duniya ta Amince da Sakacinta a Yakin Sudan

ByGlobal Tracker

May 4, 2023

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya amince da gazawar majalisar wajen dakatar da yakin da ya barke a Sudan.

A yanzu haka dai ana ci gaba da gwabza fada tsakanin janar-janar biyu da ke da karfin fada-a-aji a harkokin tsaron kasar lamarin da karara ya nuna gazawar majalisar na sulhunta tsakanin bangarorin dake gaba da juna a kasar.

Mista Antonio Guterres wanda ya bayyana haka ga manema labarai a Nairobi babban birnin kasar Kenya inda yake ziyara kan rikicin na Sudan, ya ce an yi wa Majalisar Dinkin Duniya ba zata game da rikicin, saboda abin da suka sani shine yadda wasu kasashen duniya suka wuce gaba a kokarin ganin an mika mulki ga farar hula.

Guterres ya ce, a yayin da suke jiran ganin kokarin mika mulki ga farar hula, sai kwasam suka ji fada ya barke a Sudan, kuma hakan na fitar da gazawarsu a bayyane.

KU KARANTA: Buhari ya Damuwa Kan Yakin da Ake yi a Sudan

Ya ce al’ummar Sudan basu cancancin halin da aka shiga ba, saboda dama can sun dade a tagayyare saboda son kai na janar-janar din biyu dake gwagwarmayar neman mulki.

Tun a ranar 15 ga watan Afrilu kazamin fada ya barke a manyan biranen Sudan ciki harda Khartoum fadar gwamnatin kasar, tsakanin shugaban kasar Abdel Fattah al-Burhan, wanda ke jagorantar sojoji gwamnati, da mataimakinsa da ya koma abokin gaba Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar dakarun sakai na RSF.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 550 ne aka kashe sannan wasu kuma dubu 4 da 926 suka jikkata, a cewar alkaluman ma’aikatar lafiya na baya-bayan nan.

Tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir a shekarar 2019, masu shiga tsakani na kasa da kasa suka yi ta kokarin sassanta farar hula da sojoji domin zama teburin tattaunawa.

 

RFI Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *