• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

Rundunar Yan Sandan Kano Na Neman Wanda ya Kashe Mahaifiyarsa Ruwa a Jallo

ByGlobal Tracker

May 4, 2023

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da cewa tana Neman Yaron nan Ibrahim Musa Mai shekaru 22 Ruwa a Jallo bisa Zargin sa da Kashe Mahaifiyarsa.

Kakakin rundunar Abdullahi Haruna Kiyawa wanda ya bayyana hakan ga manema labarai ya ce ana zargin Ibrahim Musa ne Mai shekaru 22 da laifin dabawa Mahaifiyarsa wuka ya kuma gudu a unguwar rimin Kebe dake yankin Karamar hukumar Nassarawa a Kano arewa maso yammacin Nigeria.

Wani likita a Asibitin kwararru na Muhammad Abdullahi Wase ne dai ya tabbatar da mutuwar matar Mai suna Hajara Muhammad Mai shekaru 50 a duniya.

KU KARANTA: Rundunar ‘Yan Sanda ta kama Isiyaku Danja Bisa Zargin Kona Ofishin INEC

A cewar Kiyawa “an sami wukar da aka aikata lefin da kuma jini a gurin da aka aikata lefin.”

“Mun tura jami’an mu da suka kware a bincike domin bibiya tare da tabbatar da an kama wanda ake Zargin,” in Kiyawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *