• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Nada Ibrahim Yaro D/tofa Talban Alajawa

ByGlobal Tracker

May 6, 2023

Sarkin Alajawa a karamar hukumar Bagwai Alhaji Abubakar M. Abubakar ya nada shugaban sashin yada labarai na Gidan Radiyon Tarayya Pyramid FM Ibrahim Yaro Dawakin Tofa a matsayin Talban Alajawa.

Jim kadan da kammala nadin sarautar a fadarsa da ke garin Alajawa a karamar hukumar Bagwai, Sarkin ya bayyana cewa nadin sarautar ya biyo bayan sahalewar Madakin Bichi Hakimin Karamar Hukumar Bagwai Alhaji Nura Shehu Ahmad bisa la’akari da irin kokarin sa a sha’anin cigaban yankin.

Sarkin ya hori wadanda aka nada da su cigaba da jajircewa wajen hidimtawa al’ummar yankin Alajawa da karamar hukumar Bagwai da ma jihar Kano baki daya.

READ ALSO: Masarautar Kano Zata Tallafawa Matuka Akori-kura Don Samun Matsuguni na Din-din-din

A zantawar sa da manema labarai jim kadan da kammala nadin Talban Alajawa, Alhaji Ibrahim Yaro Dawakin Tofa ya godewa sarkin na Alajawa bisa amincewa da shi cikin wadanda aka yi wa nadin sarautar.

Sauran wadanda aka nada akwai Umaru Magaji a matsayin Magajin Garin Alajawa da Tukur Adamu a matsayin Sarkin Yakin Alajawa da Isma’il Abubakar a matsayin Yariman Alajawa da Kuma Halilu Alhassan a matsayin Makaman Alajawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *