Kungiyar masu fataucin shanu da Dabbobi ta kasa ta bayyana cewa, ta bijiro da shirye-shirye domin inganta harkokin ya’yanta na gudanar da safarar shanu da Dabbobi zuwa kudancin kasar nan.
Shugaban kungiyar na kasa Mustapha Ali ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai anan jihar kano.
Mustapha Ali ya ce a lokutan baya duk Dan kungiyar da zai yi safarar shanu da Dabbobi zuwa jihohin kudu sai ya rike kudade wajen dubu Dari domin baiwa wasu mutane ba gaira ba dalili.
Ya kuma ce yawan kisan gillar da ake yiwa ya’yan kungiyar a kudancin Najeriya a hanyarsu ta shiga, shubancin kungiyar ya taka muhimmiyar rawa wajen dakatar da hakan wanda bai kamata cewa ana kasa daya haka ta rika faruwa ba.
Ya ce kungiyar tana tallafawa marayu wanda ‘ya’yan kungiyar suka mutu suka bari, wanda ko a karamar sallar da ta gabata sai da hukumar gudanarwa kungiyar ta yi musu dinkunan kayan sallah domin su ma su kasance cikin jindadi da walwala kamar kowa, inda kuma ya ce, Kungiyar ba za ta gajiya ba wajen taimakawa iyalan wadanda suka Rasu.
KU KARANTA: KANO: Mun Shirya Tsaf Don Nishadartar da Masu Bude Ido — Shugaban Hukumar Kula da Gandun Daji
Shugaban ya bayyana cewa yana fatan Gwamnati mai jiran Gado karkashin Shugabancin Bola Ahmed Tunubu, za ta kaiwa kungiyar dauki da bata damar data kamata domin bunkasa harkokin ‘ya’yan kungiyar a kasa baki daya.
Shugaban ya kuma ya ce kungiyar za ta ci gaba da baiwa Gwamnati cikakken hadin kan daya dace musamman wajen samarwa matasa ayyukan yi da biyan Gwamnati kudaden haraji domin ciyar da kasar nan gaba.
Haka zalika ya shawarci ‘ya’yan kungiyar da su kasance masu bin dokokin da kungiya ta sanya a gaba ta hanyar ba da cikakken hadin kan data bijiro da shi domin inganta harkokin kasuwancin su.
Ta kuma yi kira da sauran kungiyoyi da su yi koyi da kungiyar masu fataucin shanu da Dabbobi ta kasa wajen tallafawa marayu a aka mutu aka barsu.