• Tue. Jun 17th, 2025

Global Tracker

Truth and Objectivity

An Bayyana Zaben Shugaban Kasar Turkiyya a Matsayin wanda Bai Kamala Ba

ByGlobal Tracker

May 15, 2023

Hukumar zaɓe a kasar Turkiyya ta sanar da zuwa zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar bayan da Mista Erdorgan ya gaza samun kashi 50 na ƙuri`un da za su ba shi nasara.

Shugaban hukumar zaɓen ƙasar Ahmet Yener, ya ce za a gudanar da zagayen zaɓe na biyu ranar 28 ga watan Mayu, wato mako biyu mai zuwa kamar yadda doka ta tanada.

Ahmet Yener ya ce sakamakon zagayen farko na zaɓen ya nuna cewa Shugaba Erdogan ya samu kashi 49.51% na ƙuri’un da aka kaɗa.

Shi kuwa, babban jagoran ‘yan adawar ƙasar, Kemal Kilicdaroglu, ɗan takarar gamayyar jam’iyyun adawan Turkiyya, ya samu kashi 44.88% na ƙuri’un.

Mutum na uku da ke takarar Sinan Oğan na jam`iyyar NP, ya samu kashi biyar na ƙuri`un, kamar yadda hukumar zaɓen ta bayyana.

KU KARANTA: Hukumar Zabe Ta Dage Cigaba da Karbar Sakamakon Zaben Shugaban Kasa

Dokar ƙasar ta tanadi cewa dole ne sai ɗan takara ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, kafin a ayyana shi matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

A yanzu dai kallo ya koma tsakanin Erdogan da Mista Kilicdaroglu, kuma hankula sun karkata kan Sinan Ogan bisa rawar da zai iya takawa a zagaye na biyun.

Mista Ogan dai ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi ɗan takarar da yake adawa da jam’iyyar Kurɗawa tare da shirin korar ‘yan gudun hijira.

 

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *