Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi na jihar Kano Dahiru Adda’u ya bayyana kwamishinar Ma’aikatar Mai barin-gado Dakta Mariya Mahmud Bunkure a matsayin Kwararriya a fannin samar da hanyoyin bunkasa Ilimi da kuma kishin cigaban fannin a fadin jihar Kano da Kewaye.
Alhaji Dahiru Adda’u ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci Ma’aikata da sauran jama’a wajen bada lambar yabo da karrama kwamishiniyar Mai barin gado la’akarin da irin cigaban da ta kawo da jajurcewarta don ganin fanni Ilimi a Kano musamman ilimin gaba da sikandire ya samu cigaba.
A cewarsa, Dakta Bunkure Mai karbar shawarwari daga kowanne maaikaci a Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ce dukka domin farfado da kima da kuma darajar Ma’aikatar wacce ta kasance kamar sabuwa la’akari da cewa a baya ai hade ta a Ma’aikatar Ilimi lamarin da ya janyo ta Dena cin gashin kanta.
Ya Kuma bada tabbacin cewa dukkan jami’an Ma’aikatar na yi mata fatan alkhairi tare da bayyana cewa a shirye suke suyi aiki da ita a nan gaba koda ta sami wani mukamin.
KU KARANTA: Rundunar Yan Sandan Kano ta Kama Matashin da ya Kashe Mahaifiyar sa.
A jawabinta, kwamishiniyar ta yabawa jami’an Ma’aikatar bisa ganin dacewar ta, tare da bata lambar girmamawa tana Mai cewa Ma’aikatar gida ce a gurin ta kuma zata bada gudun mowa a kowanne lokaci da ake bukatar gudun mowa ko tallafin ta.
“Higher education ta zamar min kamar family ce, kuma ina fata duk abinda za’a yi a nan matukar aka gayyaceni Kuma ina nan, to insha Allah zanzo na bada gudun mowa ta, Kuma ko na tafi aka ga da akwai bukatar Karin bayani a koda yaushe a shirye nake nazo na bada gudun mowa da Karin bayani ga kowa, muna fatan wanda zai gajemu dai Dora da kawo wasu tsaren da zai kawo cigaban alummar Kano baki daya,” inji Dr. Bunkure.
Ta bayyana wasu daga cikin nasarorin da ta samu da suka hadar da daga darajar kwalejin Ilimi ta saadatu rimi dake Kumbotso zuwa Jami’ar Ilimi ta Kano, da kafa kwamitoci masu karfi domin bibiyar harkokin makarantun gaba da sikandire (‘Visitation Panels’) wanda aka yi su domin bibiya tare da bada shawarwarin da zasu tallafa wajen cigaban makarantun baki daya.
Ta kuma ce shirye-shirye sun kankama wajen daga darajar kwalejin share fagen shiga jami’a ta KARS dake kan titin ‘Airport’ zuwa kwalejin Ilimi ta jihar Kano, da kuma kokarin daga darajar kwalejin addinin musulunci da sharaa wato ‘Legal’ wacce ita da kanta zata rika bada shaidar Karatu da NCE maimakon dogara da Kwalejin saadatu rimi dake Kumbotso da kuma Jami’ar Amadu Bello dake Zaria a jihar Kaduna.
“Ko wa a higher education ba wanda bai bamu gudun mowa ba, muka samu aka daga darajar kwalejin saadatu rimi zuwa Jami’ar Ilimi, yanzu ita ce Jami’ar da take bada Ilimi ta 61 a Nigeria, sannan kuma a jami’o’i da ba na education ba, a dukkan jami’o’i a Nigeria ita ce ta 222,” inji Mariya.
Ta ce “A lokacin mu ne muka fara aiwatar da tsarin bukukuwan yaye dalibai a wasu Kwalejojin da a baya akayi sama da shekaru sama da 10 ba Yi bukukuwan yaye dalibai ba, Allah ya temake mu munyi bukukuwan a kwalejin fasaha ta Polytechnic, da Kwalejin nazarin Addinin musulunci ta ‘Legal’ da sauran wasu.”
KU KARANTA: Muna Ta Ya Kwankwaso, Abba Gida-gida da Mutanen Kano Barka da Sallah — Shafi’u Bachirawa
A wani cigaban labarin kuma, kwamishiniyar Ma’aikatar Ilimi Mai zurfi ta jihar Dakta Mariya Mahmud Bunkure ta Musuluntar da Yar sandan da take kula da lafiyar ta.
Wasu bayanai da GLOBAL TRACKER ta samu sun nuna cewa Yar sandan Mai suna Tayo yanzu ta koma Fatima.
Wata majiya da bata so a ambace ta ba ta ce Fatima na cigaba da gudanar da ayyukan ta kamar yadda ta saba Kuma kyakykyawar mu’amalar dake tsakaninta da kwamishiniyar ne yayi sanadin masuluntar ta.