Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano ta umurci shugabannin kananan masana’antu da na kasuwar Sharada da ke karamar hukumar Birnin Kano da Kewaye da su yashe magudanan ruwa gaba daya domin gujewa ambaliyar ruwa.
Babban Sakataren ma’aikatar Alhaji Aliyu Yakubu Garo ne ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci kwamitin tsaftar mahalli na jihar Kano wajen duba aikin tsaftace muhalli na kasuwanni da Ma’aikatu da hukumomin gwamnati wanda ake gudanarwa a duk jumaar karshen wata a nan Kano.
A cewarsa, magudanan ruwan biyu sun toshe gaba daya wanda hakan ke zama babbar barazana ga muhalli saboda yawan tsammanin samun ruwan sama a koda yaushe.
Babban sakataren ya ci gaba da cewa, Umarci Shugabannin Kananan Kamfanonin Sharada da su tabbatar da sun yashe magudanan ruwan su ko wanda akasin hakan ka iya kawo ambaliyar ruwa a damunar bana a yankin.
KU KARANTA: ‘Mariya Bunkure, Kwararriya Mai Kishin Ilimi a Kano’ — Dahiru Adda’u
“Magudanar ruwan su gaba daya sun toshe kuma suna fuskantar mummunar barazanar ambaliyar ruwa, don haka mun yi kira gare su da su gaggauta fara aikin share magudanar ruwa nan da mako mai zuwa, kuma mun sanya jami’an mu da su bi diddigin lamarin tare da tabbatar da sun bi umarnin da muka bayar.” Inji Aliyu Garo.
Aliyu Garo ya kuma yi kira ga mahukuntan kasuwar sharada da su gaggauta gyara duk wani abin lura da aka yi musu musamman ma tsaftataccen ruwa da kawo karshen rashin isasshen ruwa a mayankar su ta kasuwar.
Babban Sakataren ya bukaci mazauna Kano da su yi amfani da lokacin tsaftar muhallin da zaa gudanar a gobe asabar wajen yashe magudanan ruwan domin gudun afkuwar ambaliyar ruwa.